Firaministan kasar Iraq Haider al-Abadi ya roki kasashe dake yankin Gabas ta Tsakiya da su yi aiki kafada da kafada domin karfafa fafutukar da suke yi na yaki da matsalar ta'addanci.
Abadi, ya yi wannan kalamin ne a cikin wata sanarwa bayan ya gana da mataimakin firaministan kasar Kuwaiti Sheikh Sabah Al-khaled Al-Hamad Al-Sabah, wanda ya kawo ziyara aiki a kasar ta Iraqi.
Abadi ya kara da cewar, kara bunkasa tattalin arziki, tare da habbaka dankon zumunta a tsakanin kasashen dake yankin, wani abu ne da zai iya karawa jama'a karfin gwiwa tare da nesanta jama'a daga barazanar ta'addanci da tsatsauran ra'ayi.
A nashi jawabin, mataimakin firaministan Kuwaiti ya ce, kasar Iraq muhimmiyar kasa a yankin, kuma sauran kasashe a shirye suke su hada kai domin tunkarar kalubalen dake gaba. (Suwaiba)