in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan IS 43 a kusa da birnin Bagadaza
2015-01-19 10:10:18 cri

Dakarun sojin kasar Iraqi sun hallaka mayakan kungiyar IS 43, yayin wani lugudan wuta ta sama kan wasu yankunan dake wajen birnin Bagadaza.

Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron kasar ta ce, sojojin sun yi dauki ba dadi da mayakan na IS a ranar Lahadi, a yankunan hamadar Halabsa, da Nibaie, da al-Liyn, da Albu Obied da Albu Khalifa, inda suka hallaka mayakan 19 tare da kwace wuraren da suke samun mafaka.

Kaza lika dakarun sojin sun lalata makamai da motocin kungiyar da dama, sun kuma kwance wasu bama bamai 27, da mayakan suka dana a wasu hanyoyi.

A farmakin da sojojin suka kai yankin Sabi al-Bour kuwa, sanarwar ta ce, sun kashe mayakan IS 24, ciki hadda wasu kusoshin kungiyar, suka kuma lalata wasu makami da motocin mayakan. Sojojin kasar ta Iraqi sun kuma lalata wasu makaman roka, da ake kyautata zaton ana shirin amfani da su ne wajen kaiwa yankin Kadhmiyah, mai tarin mabiya darikar Shi'a hari.

Yanayin tsaro dai ya kara tabarbarewa a kasar Iraqi tun cikin watan Yunin bara, sakamakon barkewar fada tsakanin dakarun sojin kasar da mayakan 'yan tawayen Sunni, wadanda a wancan lokaci suka kwace birnin Mosul, da yankunan Nineveh tare da sauran yankunan 'yan Sunni. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China