A jiya ne dakarun tsaron kasar Iraki da mayakan kawance suka kaddamar da hare-hare guda biyu kan mayakan IS a lardunan Anbar da kuma Salahudin.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, dakarun sun samu nasarar kwace kauyuka 14 a yankin, tare da kashe mayakan na IS da dama. Sai dai majiyar ba ta yi wani karin bayani game da yawan mutanen da suka jikkata na bangarorin biyu ba.
Bugu da kari dakarun tsaron dake samun goyon bayan mayakan Shi'a da Sunni sun yi nasarar kwace wasu garuruwan da ke kusa da Duluiyah mai nisan kilomita 90 daga arewacin birnin Bagadaza, da kuma wasu garuruwan da ke kusa da Balad da Mu'tasim daga hannun mayakan na IS.
Lardin na Anbar dai ya kasance fagen daga na 'yan watanni tsakanin mayakan IS da dakarun tsaro da ke samun goyon bayan mayakan Sunni da ba sa kaunar kasancewar kungiyar ta IS mai tsattsauran ra'ayi a yankunansu. (Ibrahim)