in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar Kurdawa ta kwace iko a muhimmin gari dake arewacin Iraqi
2014-12-22 15:19:54 cri

Rundunar tsaro ta Kurdawa ta kwace kusan gaba dayan garin Sinjar dake gundumar Nineveh a arewacin kasar Iraqi.

Wata majiyar tsaro ta kasar da kuma shafin kafar Internet na jam'iyyar damokradiyya ta Kurdawa KDP sun ce, nasarar da aka samu ta biyo bayan dakarun tsaro na Iraqi sun samu galabar kutsa kai cikin garin na Sinjar, inda ake yaki ba kakkautawa tsakanin Kurdawan da kungiyar musulunci ta ISIS.

Majiyar jam'iyyar ta KDP ta ce, an ci gaba da jin karan bindigogi da fashewar wasu abubuwa a Sinjar a yayin da dakarun Kurdawa wadanda ake kira 'Peshmerga" suke bata kashi da kungiyar ISIS a fafutukar da suke yi na ceton wasu unguwanni dake garin na Sinjar daga hannun 'yan kungiyar islama ta ISIS.

Majiyar ta ce, an tabka gumuzu na baya-bayan nan a wani wuri dake da nisan kilomita 100 a yammacin babban birnin gundumar Nineveh, Mosul.

Majiyar ta ce, wata tawagar kwararru masu kwance bama-bamai sun kwance wasu nakiyoyi da aka dasa a gefen hanyoyi.

Wata majiyar tsaro ta Kurdawa ta shaida wa kamfanin dillanci labarai naXinhua cewar, dakarun Kurdawan sun samu nasarar kwato unguwanni da dama dake tsakkiyar Sinjar, wadanda suka hada da wani gini na gwamnati, wanda a yanzu Kurdawan suke amfani da shi a matsayin wurin da suka girka tutar yankin Kurdawa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China