Dan majalisar dokokin kasar Birtaniya, Charles Powell ya bayyana cewa, sa kaimi ga batun gudanar da harkokin kasa bisa doka, wani babban ci gaba ne da Sin ta samu a fannin kafa dokoki. A yayin da Sin ke zurfafa gyare-gyare, dole ne Sin ta kara inganta rawar da dokoki ke takawa. Ya ce, wannan babban masomi ne na Sin wajen kyautata dokokin kasar.
Babban manazarci dake aiki a hukumar Brookings ta Amurka, Kenneth Liberthal ya bayyana cewa, wannan cikakken zaman taro ya kasance taro na farko da JKS ta dauki 'gudanar da harkokin kasa bisa doka' a matsayin babban taken taron. Rahoton taron ya bayyana hanyar da Sin za ta bi wajen samun ci gaba, da kokarin kasar na kyautata dokoki da kara sa haske a ciki, domin kaucewa sa hannu da wasu kungiyoyi da jami'ai za su yi. Wannan cikakken zaman taro ya samar da sabon karfi da sabuwar hanya wajen cimma wannan buri cikin yakini.(Fatima)