Sharhin ya ce, A yayin taron kungiyar kula da aikin zurfafa gyare-gyare na kasar Sin, babban sakataren JKS mista Xi Jinping ya taba bayyana cewa, ya kamata a gudanar da aikin yin kwaskwarima daga dukkan fannoni bisa doka. Wanda yake burge sauran kasashen duniya sosai.
An mai da batun gudanar da harkokin kasa bisa doka a matsayin wani muhimmin mataki cikin manyan tsare-taren gudanar da harkokin kasar Sin, wanda ya sheda saurin ci gabansa. Bugu da kari, an hada shugabancin JKS da ikon jama'a kana da gudanar da harkokin kasa bisa doka yadda ya kamata, baya ga hada aikin gudanar da harkokin kasa bisa doka da da'a, duk wadannan sun amsa tambaya kan dangantaka a tsakanin shugabancin jam'iyyar da batun gudanar da harkokin kasa bisa doka. Haka zakila, an tabbatar da muhimmin matsayin JKS na shugabancin sha'anin gurguzu mai tsarin musamman na Sin, baya ga jaddada muhimmancin tsayawa tsayin daka kan shugabancin jam'iyyar don gudanar da harkokin kasa bisa doka, gami da muhimmancin dogaro bisa aikin gudanar da harkokin kasa bisa doka don ci gaban shugabancin jam'iyyar. Yanzu JKS da ke kan karagar mulki tana ta samun kyautatuwa ta hanyar kara fahimtar batun gudanar da harkoki bisa doka.(Kande Gao)