An bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da JKS ta bayar a karshen wata ganawa da kwamitin tsakiya na hukumar kula da harkokin siyasa ya gudanar a yau, inda aka nuna irin matakan da ake dauka wajen magance batun cin hanci da rashawa.
Bugu da kari sanarwar ta ce, kamata ya yi a kara daukar matakai game da matsayin da jam'iyya ke dauka kan manyan jami'ai da mambobin jam'iyya na bin dokoki kamar yadda aka tsara.
Taron wanda shugaba Xi Jinping ya jagoranta ya kuma tsayar da ranar 12 zuwa 14 ga watan Janairu a matsayin ranakun da za a gudanar da taro na 5 na hukumar ladabtawar da jam'iyya karo na 18. (Ibrahim)