in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana ta yin kokarin yaki da cin hanci da rashawa
2014-10-26 17:21:28 cri
An kira taro karo na hudu na kwamitin sanya ido wajen ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 a jiya Asabar 25 ga wata a nan birnin Beijing, inda zaunannen wakilin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS, kana darektan kwamitin sanya ido wajen ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta Sin, Wang Qishan ya jaddada cewa, kasar tana ta yin kokarin bunkasa jam'iyyar kwaminis ta Sin da yaki da cin hanci da rashawa.

Wang Qishan ya ce, cikakken zaman taro na hudu na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 wani muhimmin taro ne da aka yi a yunkurin bunkasa mulkin gurguzu irin na salon musamman na kasar Sin. 'kudurin kwamitin tsakiya na JKS kan manyan batutuwa dangane da sa kaimi wajen gudanar da harkokin kasa bisa doka daga dukkan fannoni' da aka zartas a gun taro, wani muhimmin mataki ne da aka fitar a fannin gudanar da harkokin kasa bisa doka

Ban da haka, Wang Qishan ya kara da cewa, yanzu muna ci gaba da fama da matsalolin bunkasa JKS da yaki da cin hanci da rashawa, dole ne mu yi hakuri, da kara kwarin gwiwa wajen kara karfin yaki da cin hanci da rashawa, da zummar fitar da wani tsari mai amfani sosai a wannan fanni.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China