Ganin kasar Sin ke rike da shugabancin kwamitin na karba karba na wannan watan Fabrairun, ta bada shawarar zaman mahawara na bainin jama'a a litinin mai zuwa karkashin taken kula da zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa don waiwaiye akan tarihi da kuma jaddada muhimmancin da ka'idojin kundin majalissar, inji Madam Hua.
Wannan shekarar ce za'a cika shekaru 70 da kafa majalissar sannan kuma da nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu.
Muhawarar zai bada damar da bangarori da dama su waiwayi tarihi su kuma hangi gaban su tare da bayyana ma Duniya duniya shawarar majalaissar na kare zaman duniya da tsaro.