Wang Min wanda ya bayyana hakan cikin jawabin sa ga taron kwamitin raya zamantakewar al'umma na MDD, ya kara da cewa kasashen duniya na fuskantar sabbin kalubale, da matsaloli, a kokarin su na bunkasa zamantakewar al'umma.
Ya ce, ya dace a sa kaimi ga bunkasar zamantakewar al'ummar duniya cikin adalci da cimma moriyar juna, da kiyaye muhalli, da samun bunkasuwa mai dorewa, da binciko sabbin dabaru, da hakuri da juna, a lokacin da ake kara samun bunkasar zamantakewar al'ummacikin daidaituwa.
Haka zalika, Wang Min ya bayyana cewa, Sin ta yi imani da kara samun ci gaba a sha'anin samun bunkasuwa, ciki har da fannin zamantakewar al'umma. Har wa yau za ta ci gaba da more fasahohin ci gaba tare da sauran kasashen duniya, da kara samar da damar hakan ga duniya, domin samun wadata a kasar Sin da ma duniya baki daya. (Zainab)