Kasar Tanzaniya ta gaggauta tsarinta na kafa wata gidauniyar kare muhalli dake nauyin kare muhallin tsaunukan Kilimandjaro da Meru, dukkansu dake arewacin kasar. Ministan albarkatun kasar Tanzaniya da yawon bude ido, Lazaro Nyalandu ya bayyana a ranar Laraba cewa, wannan dabara na cikin tsarin nauyin dake wuyan gwamnati na kare tsaunin Kilimandjaro, wani dutsen Afrika mafi tsayi na mita 5.895, da kuma dutsen Meru wanda shi ne dutse mafi girma na biyu a kasar Tanzaniya kuma na biyar mafi tsayi a Afrika tare da tsawon mita 4.565. Albarkatu, har da taimakon jama'a da na kudi, ina bukatarsu idan muna fatan sake dasa itatuwa sosai a cikin kasarmu. Za mu iyar shiga wannan aiki gaba dayanmu, in ji minista.
Wannan sabon ci gaba ya zo daidai lokacin da wannan tsaunukan biyu dake yankin Southern Highland a gabashin Tanzaniya suka samu wani asusun kansu, wato asusun taimako domin kiyaye tsaunukan dake gabashin kasar (EAMCEF).
Ministan ya mayar da dutsen Kilimandjaro da dutsen Meru a matsayin wani shaton ruwan kasa dake samar da ruwa ga al'ummomin dake rayuwa nesa da kusa da wadannan tsaunuka. (Maman Ada)