Yanzu a nan kasar Sin, tare da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin sauri, ana fama da matsalar gurbatan muhalli sosai a kauyuka, abin da ya sa wasu daga cikin su suna kewaye da shara, yayin da gurbataccen ruwa ke bazuwa a ko ina a sakamakon kiwon dabbobi, sannan maganin kwari a gona ya gurbata yankunan gonaki sosai. A kokarin daidaita wannan matsala, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, gwamnatocin mataki mataki na Sin suna ta kokarin kyautata muhalli a kauyukan kasar.
Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, ya zuwa karshen shekaru 2013, baki daya an kebe kasafin kudi yuan biliyan 19.5 domin kiyaye muhalli na kauyuka, yayin da gwamnatocin mataki mataki suka zuba jari sama da yuan biliyan 26 a wannan fanni, domin nuna goyon baya ga kauyuka dubu 46 wajen kyautata muhalli. Mutanen kauyuka sama da miliyan 87 sun ci gajiya. An yi kiyasin cewa, za a kara zuba jari kan wannan fanni a bana.(Fatima)