Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce, ta samar da daftarin doka da wani muhimmin tsari domin daukar matakai a kan kayayyakin lantarki da suka lalace a cikin kasar ta Nigeria.
Ministan harkokin muhalli ta Nigeria Laurentia Mallam, wacce ta bayyana hakan ga wani dandalin taro na kasashe da ke aiki tare da Nigeria ta ce, gwamnatin Nigeria ta jajurce domin kulawa da barazanar dattin kayayyakin lantarki ko na'urori.
Nigeria na daya daga cikin kasaashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar duniya kan tunkarar hanyoyin da za'a bi domin kawar da datti masu dauke da gurbataccen abu.
Ministar ta ce, yarjejeniyar ta haifar da nasarori wajen kulawa da gurbataccen datti na yau da kullun.
Kamar yadda ministrar ta bayyana, masana'antun laturonic da na fasahar yada labarai na daya daga cikin masana'antun dake samun habbaka a duniya.
A halin da ake ciki, kwamfutoci da sauran kayayyaki lantarki na ci gaba da haddasa matsala a wajen hanyoyin kawar dattin su idan sun lalace. (Suwaiba)