in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na shirin mayar filayen gonaki zuwa gandun daji kimanin eka miliyan 10
2015-01-05 15:50:59 cri
Bisa labarin da aka samu daga taron shugbannin hukumomin kula da aikin daji na kasar Sin a ran 5 ga wata, an ce, kasar Sin na shirya mayar da karin gonaki zuwa gandun daji kimanin eka miliyan 10 a shekarar 2015, kuma za ta fara mayar da gonakin dake fuskantar kwararowar hamada da gonaki na gangara dake mafarin ruwa da su zama gandun daji.

Sabon zagaye nan na mayar da karin gonaki da su zaman gandun daji na da muhimmiyar ma'ana wajen kyautata muhalli, zaman rayuwar al'umma, da kuma tattalin arzikin kasar. Mataimakin shugaban hukumar kula da aikin dajin kasa ta Sin Zhang Jianlong ya bayyana haka ne a yayin taron, ya kuma kara da cewa, a shekarar bana, za a ci gaba da karfafa ayyukan da abin ya shafa, da kuma inganta sakamakon da aka samu dangane da aikin nan na mayar da gonaki da su zama gandun daji.

Bugu da kari, ya ce, a shekarar 2015, babban makasudin hukumar kula da aikin daji shi ne habaka yankin daji da kuma karfafa ayyukan daji bisa doka, kiyaye gandun daji, fadama da dai sauransu.

Kana, bisa labarin da aka samu, hukumar aikin daji ta tsakiya ta zuba yuan biliyan 151.7 kan harkokin daji a shekarar 2014, inda ta kammala gina yankunan daji eka miliyan 90.41, da suka hada da lambun shan iska na gandun daji, wurin shan iska na fadama, wurin sha iska na hamada da kuma yankin kiyaye muhallin halittu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China