Ofishin kungiyar kawancen kiyaye halittu ta kasa da kasa ko IUCN a takaice, ta sanya wasu wurare 6 dake nan kasar Sin, cikin jerin wuraren kiyaye halittu a rukuni na farko.
Game da hakan, babban jami'in a ofishin kiyaye halittu Feng Jiaping, ya ce wannan jadawali na IUCN, ma'auni ne da ake amfani da shi a dukkanin fadin duniya, wajen tantance yadda ake kula da wuraren kiyaye halittu.
Don haka shigar da wadannan wurare 6 na kasar Sin cikin jerin sunayen na IUCN, tamkar yabo ne ga yadda kasar ta Sin ke gudanar da aikin kiyaye halittu.
Mista Feng ya kara da cewa, har kullum gwamnatin Sin na mai da hankali kan ayyukan kiyaye halittu. Kuma ya zuwa wannan lokaci, akwai yankunan kiyaye halittu har 2697, da dazuka dake matsayin wuraren shan iska 2948, da wuraren shan iska dake fadamu guda 916. Sauran sun hada da wuraren yawon shakatawa, da wuraren shan iska da ke da halin musamman na kasar Sin, da sauran nau'o'in wuraren kiyaye halittu daban daban, a sassan fadin kasar Sin.
Ya ce fadin wadannan wuraren kiyaye halittu, ya zarce kashi 18 cikin dari bisa jimillar fadin kasar Sin baki daya. Kuma kasancewar wuraren kiyaye halittu masu yawan albarkatu da kamanni daban daban, kasar Sin za ta zama misali na musamman a fannin tinkarar kalubalen da ake fuskanta wajen kiyaye halittu ga dukkanin sauran kasashen duniya. (Tasallah)