in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da kokarin farfado da al'ummar kasar Sin
2015-02-25 15:42:50 cri

Babu wani manzancin da ya fi alfahari bisa farfado da wata al'umma, kuma babu wani sha'ani da ya fi muhimmanci sama da cimma burin jama'a da yawansu ya kai sama da biliyan daya. Yanzu haka ana ci gaba da kokarin farfado da kasar Sin a fannoni daban daban. 

Wannan wani sabon masomi ne. A watan Nuwamba na shekarar 2012, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kwamitin tsakiyar JKS ya karbi ikon mulkin kasa daga tsoffin jami'an kasar Sin, inda suka ci gaba da kokarin neman samun farfadowar al'ummar kasar Sin bisa yunkurin JKS, da jama'ar kasar tun bayan kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar ta Sin, a kokarin samun karin ci gaba a wannan fanni.

A dakin adana kayan tarihi na kasar Sin, ana bikin nune-nune mai taken "Hanyar samun farfadowa", inda aka yi la'akari da yadda za a samu karin bunkasuwa. A tudun Lianhua dake birnin Shenzhen, a gaban mutum-mutumin marigayi Deng Xiaoping, an sami babban ci gaba tare da yin kwaskwarima a can. Domin tunawa da gudanar da kundin tsarin mulkin kasa a ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 1982, an nanata gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, tare da girmama dokoki.

A wata na farko da sabuwar gwamnatin kasar ta karbi mulki, ta kafa burin da take fatan cimmawa. A cikin shekaru biyu da suka wuce, a yayin babban taron JKS karo na 18, an jaddada cewa za a kammala kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa, a kuma yayin cikakken zama na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, an kokarta zurfafa yin kwaskwarima, a yayin cikakken zama na hudu na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 kuwa, an bukaci gudanar da harkokin gwamnatin kasa bisa dokoki da sauransu. Dukkanin wadannan matakai sun bayyana cewa, ana samun kyautatuwa bisa manyan tsare tsare daga fannoni hudu.

Tarihi ya kan bayyana gaskiya. Ko da yake jimillar kudin da kasar Sin ke samu yana kan sahun gaba, a daya hannun al'ummar kasar ta Sin da dama na ci gaba da fama da talauci.

Bisa matsin lambar gurbatar muhalli, ana kokarin canza hanyar samun bunkasuwa. Dadin dadawa, ana bukatar samun ci gaba cikin sauri, yayin da ake rashin karfin samar da sabbin kayayyaki. Kasar Sin tana fuskantar babbar matsalar tabbatar da tsaro a cikin gida da kuma ketare.

Shugaba Xi na la'akari da dukkanin wadannan matsaloli bisa kimiyya da fasaha, kuma ya tabbatar da amincewa da juna, da samun fasahohi daga hakikanin yanayin da Sin ke ciki, da kokarin daidaita matsalolin da Sin ke fama da su. A sabili da haka, ya gabatar da shirin samun kyautatuwa bisa manyan tsare-tsare a fannoni hudu, bisa hakikanin bukatun samun bunkasuwar kasar, da bukatun jama'ar kasar, a kokarin sa kaimi ga daidaita wadannan matsaloli.

Game da hakan a karo na farko an kafa kudurin "kammala kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa" a matsayin muhimmin mataki na cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin. A karo na farko an dauki "kyautata da bunkasa tsarin gurguzu mai alamar kasar Sin, da zamanintar da tsari da karfin gudanar da harkokin kasa", a matsayin babban burin zurfafa yin kwaskwarima a kasar.

A karo na farko an hada batun "gudanar da harkokin kasa" da "zurfafa yin kwaskwarima" a gu daya. Kuma a karon farko an tabbatar da hanyar kyautata jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yadda ya kamata. Wadannan fannoni hudu dake cikin shirin suna taimakawa juna, da sa kaimi ga juna, da samun moriyar juna.

A shekaru biyu da suka gabata, an gudanar da kwaskwarima lami lafiya, tare da daukar matakai bisa babban karfi, a sabili da haka, tattalin arziki na bunkasa yadda ya kamata. Bayan haka, ana kokarin sa kaimi ga gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, tare da mai da hankali kan samun adalci, da yaki da cin hanci da rashawa. A sabili da haka, ana kokarin cimma burin Sin da na Asiya, har ma na duniya baki daya.

Yanzu muna fuskantar tarin kalubaloli a gabanmu. Za mu yi fama da batutuwan kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa, da yin kwaskwarima, da gudanar da harkokin kasa bisa doka da sauransu. Yayin da muke tafiya kan hanyar farfado da al'ummar kasar Sin, muna iya ganin cewa, a da, Sin ta sha wahalhalu da dama tare da samun nasarori, a yanzu, Sin tana samun bunkasuwa cikin sauri, a nan gaba kuma, za ta samu karin ci gaba tare da samar da makoma mai kyau. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China