in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya bayyana manufar tattalin arzikin kasar a dandalin Davos
2015-01-22 16:55:13 cri

An kaddamar da taron shekara-shekara karon 45 na dandalin tattalin arzikin duniya a garin Davos na kasar Switzerland a Laraba 21 ga wata. A wajen bikin kaddamar da taron, firaministan kasar Sin mista Li Keqiang ya yi jawabi, inda ya bayyana sabuwar manufar kasar Sin a fannin tattalin arziki.

Jawabin shugabannin kasashe daban daban wadanda suka halarci taron, ya kasance aiki mafi muhimmanci da ake gudanarwa a dandalin Davos, wanda ake gudanarwa a ko wace shekara. A wannan karo, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya fara jawabinsa ne da yabawa muhallin garin Davos, ya ce,'Na hau wani dutse dake dab da garin Davos, inda na hangi garin, wanda ya kasance wani irin muhalli mai ni'ima, da kwanciyar hankali. Sai dai duniyar da muke ciki ba ta cikin kwanciyar hankali a halin da muke ciki, don haka akwai bukatar daidaita dabarunmu na fuskantar sabon yanayi.'

Yanayi na rashin kwanciyar hankali da firaministan ya ambata, ya shafi yanayin siyasa na kasa da kasa, gami da bangaren tattalin arzikin duniya. Musamman ma a shekarun baya, yayin da al'ummar duniya suke sa lura kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, wasu na damuwa game da cewa, mai yiwuwa raguwar saurin ci gaban tattalin arzikin Sin, da canjin tsarin tattalin arzikinta za su haifar da illa ga tattalin arzikin kansu. Dangane da haka, firaministan kasar Sin ya yi amfani da dandalin Davos, don bayyanawa duniya sabuwar manufar kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, ya ce,'Tattalin arzikin Sin na fuskantar wani sabon yanayi, inda saurin ci gaban sa ya dan ragu zuwa wani matsakaicin matsayi, yayin da ingancin tattalin arzikin a daya bangare ke samun ci gaba. Saboda haka mun dau niyyar yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasarmu.'

A cewar Li Keqiang, dalilin da ya sa saurin ci gaban tattalin arzikin Sin ya dan ragu, shi ne tsarin tattalin arzikin duniya na samun babban sauyi, sa'an nan ci gaban tattalin arzikin Sin shi ma ya kai wani matsayi, mai tasiri ga saurin ci gaban tattalin arzikin. Yanzu tattalin arzikin kasar Sin ya kai matsayi na biyu a duniya. Wanda ko da ya yi karuwa da kashi 7% a ko wace shekara, karin adadin da aka samu a shekara guda, zai kai fiye da dalar Amurka biliyan 800, wanda ya fi kudin da aka samu bisa karuwar tattalin arziki na kashi 10% shekaru 5 da suka wuce.

A shekarar 2015, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da fuskantar matsin lamba, wadda za ta hana shi samun karuwa. La'akari da wannan yanayin da ake ciki, abun tambaya shi ne, ko za a nemi raya tattalin arzikin cikin sauri a cikin dan lokaci? Ko za a tabbatar da ci gaban tattalin arziki cikin matsakaicin sauri, tare da kokarin inganta tsarin tattalin arziki? Ba shakka za a dauki manufa ta baya. Saboda ta haka ne kawai za a iya tabbatar da karuwar tattalin arziki cikin sauri da dacewa, yayin da a sa'i daya za a daidaita tsarin tattalin arzikinsa ta yadda zai kasance mai inganci.

Ban da haka, firaminista Li ya yi alkawarin daukar matakai don magance hadari a fannin hada-hadar kudi. Ya ce, 'Muna kokarin daukar wasu takamaiman matakai, don magance fuskantar boyayyen hadari a fannin cin bashi da hada-hadar kudi. Yayin da a wani bangare na daban muke sa kaimi ga gyare-gyaren da ake yi, kan tsarin hada-hadar kudi na kasarmu. Abin da nake so in gaya muku shi ne, ba za a fuskanci wani babban hadari a bangaren hada-hadar kudin kasar Sin ba, kana sauyawar tsarin tattalin arzikin kasar Sin ba zai gamu da matsala ba.'

A cewar firaminista Li Keqiang, domin ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba ba tare da samun matsala ba, ya kamata a yi dogaro kan gyare-gyare, da daukar sabbin fasahohi, baya ga yin amfani da ikon gwamnati, da bukatar kasuwanni don kara kyautata yanayin tattalin arzikin kasar. Wannan manufa na nufin a wani bangare, za a mai da hankali kan bukatun kasuwanni, don tabbatar da yadda za a rarraba albarkatu. Sa'an nan a dayan bangaren kuma, za a sanya gwamnati ta kara taka rawa mai muhimmanci wajen tsara manufofin da za su sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China