150126-an-fara-gina-layin-dogo-da-ya-hada-mombasa-da-nairobi-bello.m4a
|
A watan Mayun bara, mista Li Keqiang, firaministan kasar Sin, ya ziyarci kasar Kenya, inda ya kulla yarjejeniya tare da shugaba Kenyatta kan yadda za a yi hadin gwiwa wajen gina wani layin dogo a tsakanin Mombasa da Nairobi. Daga bisani, an fara aikin gina layin dogon a ranar 1 ga watan Janairun bana. Aikin nan da kamfanin CRBC na kasar Sin ke kula da shi, ya kasance daya daga cikin manyan ayyukan raya kasa da kasar ta Kenya ta tsara har zuwa shekarar 2030, haka kuma yana cikin ayyukan hadin gwiwa da kasar Sin da kasashen Afirka suke kokarin aiwatarwa don gina karin layin dogo, da hanyoyin mota, gami da hanyoyin jiragen sama tsakanin kasashen Afirka.
Sai dai ganin yadda layin dogon zai ratsa shahararren wurin shakatawa na Tsavo West, ya sa mutane da yawa ke damuwa kan cewar ko aikin zai yi illa ga muhalli da zaman halittu a kasar Kenya? Dangane da tambayar, mista An Aijun, babban injiniya mai kula da aikin gina layin dogon, ya yi amsa kamar haka.
'Dukkan ayyukan da muke gudanarwa, an riga an sa kwararru a fannin muhalli su yi bincike a kansu, don haka suna kunshe da wasu fasahohin zamani na kiyaye muhalli. Ga misali, don tabbatar da cewa dabbobi za su iya kaura yadda suka ga dama a cikin wurin shakatawa na Tsavo West, mun yi shirin gina wasu burtololi, wadanda dabbobi za su iya binsu don ratsa layin dogon da muke gina. Sa'an nan, bayan da muka kammala aikin gini, za mu rufe dukkan filayen da muka yi aiki a kai da ciyayi da itatuwa.'
Kudin gina layin dogon tsakanin Mombasa da Nairobi zai kai dalar Amurka miliyan 3800, wanda kashi 90% daga cikin kudin ya kasance rancen kudin da bankin shigi da fici na kasar Sin ya bayar, yayin da gwamnatin kasar Kenya ta samar da sauran kashi 10%. Ana amfani da fasahohin kasar Sin da ma'aunin kasar wajen gina layin dogon, kana za a kammala kashi 50% na aikin cikin shekarar bana, wanda ake shirin gama shi baki daya a shekarar 2017. Dangane da wannan aiki, Jeremiah Kianga, babban darektan kamfanin layin dogo na kasar Kenya, ya ce yana da ma'ana matuka ga kasar ta Kenya.
'Aikin yana da muhimmanci sosai a fannin cigaban aikin gina layin dogo a kasar Kenya, gami da cigaban tattalin arzikin kasar. Saboda kowa ya sani, layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi zai kasance sabon layin dogo na farko da aka gina a kasar Kenya cikin shekaru 100 da suka wuce. Kana wannan aikin, yayin da ake kokarin gina shi, zai sa yawan kudin kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar Kenya GDP ya karu da kashi 2% a kowace shekara.'
Yanzu a dab da sabon layin dogon da ake ginawa, akwai wani tsohon layi wanda ya kasance layin da aka gina shekaru fiye da 100 da suka wuce yayin da kasar Kenya ke karkashin mulkin mallaka. A cewar mista Kianga, har yanzu ana amfani da tsohon layin, sai dai saurin tafiyar jirgin kasa kan wannan layi bai wuce kilomita 60 a awa daya ba, ta la'akari da yadda layin ya cika kwane-kwane, kana na'urar sarrafa layin ita ma ta tsufa sosai. Amma bayan da aka kammala gina sabon layin dogon, saurin tafiyar jirgin kasa mai dauke da fasinjoji kan layin zai kai kilomita 120 a awa daya, yayin da saurin gudun jirgin kasa mai dauke da kayayyaki zai kai kilomita 80 a awa guda. Ta haka, lokacin da ake bukata domin a tashi daga Mombasa a tafi Nairobi zai ragu zuwa awa hudu da rabi, yayin da lokacin jigilar da kayayyaki zai ragu zuwa awa 8.
Ban da haka kuma, a cewar mista Wen Gang, babban darektan kamfanin gini na CRBC na kasar Sin, karuwar saurin jigilar da kayayyaki za ta amfanawa tattalin arzikin kasar Kenya, yayin da aikin gina layin shi ma zai samar da karin guraben aikin yi ga jama'ar kasar Kenya, lamarin da zai sassanta yanayin da jama'ar kasar ke fuskanta na karancin ayyukan yi.
'A yayin da muke gina wannan layin dogo, za mu bukaci ma'aikata 'yan kasashen Afirka kimanin dubu 30 a wani lokacin da muke bukatar ma'akata sosai, hakan zai taimakawa kokarin daidaita matsalar karancin aikin yi a kasashen Afirka. Haka zalika, abin da ya fi muhimmanci shi ne, yadda wadannan ma'aikata 'yan kasashen Afirka suke aiki tare da wasu kwararrun ma'aikata na kasar Sin zai sa suka samu ci gaba sosai a fannin fasahar aiki. Sa'an nan horon da za mu yi wa ma'aikatanmu 'yan kasashen Afirka, shi ma zai sa su karu sosai a fannin mallakar fasahohin zamani, hakan zai sa su bar damuwa a fannin neman aikin yi a duk tsawon rayuwarsu.'
Kamar yadda aka tsara, layin dogon da ake ginawa zai hada Kenya, Tanzaniya, Uganda, Rwanda,Burundi da Sudan ta Kudu, wanda yake da muhimmanci sosai ga kokarin hada yankunan gabashin Afirka da hanyoyi, gami da shirin dunkule wadannan kasashe waje daya. (Bello Wang)