in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban tawagar jami'an diplomasiyyar Sin a kungiyar AU na farko zai soma aiki a wata mai zuwa
2015-02-06 16:32:12 cri

A 'yan shekarun da suka wuce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na samun saurin bunkasuwa a dukkan fannoni, kana bangarorin biyu suna samun sakamako mai kyau, game da hakikanin hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A kuma watan Mayu na shekarar bara, a yayin da yake ziyara a hedkwatar AU, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sanar da cewa, za a kafa tawagar jami'an diplomasiyyar kasar Sin na kungiyar AU, da nufin karfafa matsayin hadin kai a tsakanin Sin da Afirka. A kuma baya bayan nan kasar Sin ta soma aiwatar da aikin kafa wannan tawaga ba tare da bata lokaci ba.

A jiya Alhamis, a karon farko, jakadan kasar Sin dake AU na farko ya gana da manema labaru, inda ya bayyanawa kasashen ketare yadda aikin tawagar zai gudana.

Wannan tawaga ta kasance muhimmiyar hukuma ta daban, wadda kasar Sin ta kafa a ketare bayan ta kafa tawagogin jami'an diplomasiyya a MDD, da kungiyar hadin kan turai ta EU, da ta kungiyar nahiyar Asiya da dai sauran kungiyoyi. Kaza lika tawagar jami'an diplomasiyyar za ta zamo irin ta ta farko da Sin ta kafa a nahiyar Afirka.

A jiya Alhamis shugaban tawagar jami'an diplomasiyyar Sin a AU na farko, jakada Kuang Weilin, ya gana da manema labaru na gida da na waje a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin.

Kuang Weilin wanda haifaffen birnin Shanghai ne, kwararre ne a fannin harkokin diplomasiyya, ya kuma kasance cikin ayyukan diplomasiyya har tsawon shekaru 30. A baya ya taba aiki a sashen watsa labaru, da sashen tsara manufofi na ma'aikatar harkokin wajen kasar, kana ya yi aiki a wasu kasashe kamar Burtaniya, da Amurka da dai sauransu. Haka zalika Kuang Weilin ya taba zaman jakadan kasar Sin a kasar Saliyo. Don haka ana iya cewa yana da kwarewa sosai game da harkokin kasashen Afirka.

A matsayinsa na jakadan farko da gwamnatin kasar Sin ta nada a kungiyar AU, Kuang Weilin ya bayyana farin ciki da alfahari da wannan dama, a sa'i daya kuma ya amince da babban nauyin dake wuyansa game da cimma nasarar wannan aiki.

Jakadan na Sin ya ce har kullum, kasar Sin na bin manufar cika alkawarin da ta dauka kan hadin kai tsakaninta da kasashen Afirka. Ya ce bayan da firaminista Li Keqiang ya sanar da kafa tawagar jami'an diplomasiyya a AU a watan Mayun bara, ba tare da jinkiri ba kasar Sin ta soma gudanar da aikin tabbatar wannan manufa, kuma yanzu haka dukkanin ayyukan da suka shafi wannan manufa na gudana yadda ya kamata.

Jakada Kuang ya kara da cewa,

"Tun a karshen shekarar bara, ma'aikata na jerin farko masu aikin kafa tawagar suka isa Addis Ababa fadar gwamnatin kasar Habasha, birnin da yake matsayin helkwatar hedkwatar kungiyar ta AU, kuma ni ma zan isa birnin domin fara aiki a wata mai zuwa. Muna shirin kafa sassa daban daban domin kula da harkokin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da zaman lafiya, da tsaro da dai sauransu, dukka dai da nufin sanya sabon kuzari ga hadin kai, da cudanya tsakanin Sin da AU a dukkan fannoni. Ni da dukkan ma'aikatan tawagar, za mu yi iyakacin kokari wajen hada kai da AU, don gudanar da ayyuka yadda ya kamata."

A shekarun baya, kasar Amurka da Turai, sun kafa tawagogin jami'an diplomasiyya a AU, kuma sau da yawa AU ta bayyana burin ta na ganin kasar Sin ita ma ta kafa tawagarta a ofishin na AU.

Gamme da hakan, jakada Kuang Weilin ya bayyana cewa, baya ga kasancewar wannan mataki mai ma'anar gaske a tarihin dangantakar dake tsakaninta da kungiyar AU ba da kasar Sin, a hannu guda hakan wani muhimmin mataki ne na bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

A 'yan shekarun da suka wuce, dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar AU na samun karin ci gaba. Kuma abun lura ma a nan shi ne, hadin kan dake wanzauwa tsakanin bangarorin biyu a fannin tsare-tsare guda uku, da suka hada da samarwa kasashen Afirka layukan dogo na zamani, da tagwayen hanyoyin mota, da kuma bunkasa sufurin sama na yankuna, baya ga habaka harkokin masana'antu, yana samar da wani karfi na musamman ga manufar bunkasar nahiyar Afirka.

Bisa ayyuka da tawagar jami'an diplomasiyyar Sin za su ta yi, ko wanemene ne irin burin da Sin din ke fatan cimmawa a nan gaba, wajen bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Afirka? ga abun da Kuang Weilin ke cewa,

"Kasar Sin za ta yi kokarin tabbatar da nasarar manufofin da shugaba Xi Jinping, da firaminista Li Keqiang suka ayyana yayin ziyararsu a Afirka, za kuma ta kara cudanya da hadin kai a fannoni daban daban tsakanin bangarorin biyu, tare da kuma lalubo sabbin hanyoyin hadin kai ta fuskokin zaman lafiya da tsaro, da al'adu, da yaki da talauci, da kiwon lafiya, da kuma inganta albarkatun dan Adam da dai sauransu.

Kana kasar ta Sin za ta kara goyon bayan ta ga harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda dangantakar dake tsakanin Sin da AU, za ta zamo tamkar jagora ga dangantakar dake tsakanin Sin da daukacin nahiyar Afirka."(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Sin ta kafa tawagar wakilanta a kungiyar AU 2015-02-05 20:46:56
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China