in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin bayar da lambobin yabo ga daliban Najeriya wadanda suka yi zane-zanen kasar Sin a Abuja
2015-02-05 15:45:09 cri

Ranar Laraba 4 ga wata ne, a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya,aka yi wani biki don karrama daliban makarantun firamare da sakandare na Abuja, wadanda suka samu nasara a gasar yin zane-zane na kasar Sin.

Bikin wanda ya gudana a cibiyar al'adu kasar Sin dake Abuja, ya samu halartar babban jami'in kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da uwargidan jakadan kasar Sin dake Najeriya, da kuma wakilan dalibai da malamai daga makarantun sakandare 13 na Abuja.

 

Daga cikin dalibai 63 wadanda suka hala

rci wannan gasa, ta yin zane-zanen kasar Sin bisa taken bikin bazara, akwai dalibai guda 6 wadanda suka samu lambar yabo.

Daya daga cikin manyan alkalan gasar, kana shahararren mai yin zane-zane a Najeriya malam Muhammed Suleiman ya bayyana ra'ayinsa game da wannan gasa.

Shi kuma a nasa bangaren, wani malami da ke koyarwa a makarantar sakandaren jeka da dawo ta yaran sojoji dake Asokoro na Abuja, wato Mista Ejisun Emmanuel ya bayyana farin-cikinsa ne, saboda yadda daliban makarantarsa suka fahimci kyawawan al'adun kasar Sin. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China