in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta nuna matukar rashin jin dadinta game da samar da mafakar siyasa ga Snowden da Rasha ta yi
2013-08-02 11:06:34 cri
Fadar gwamnatin Amurka ta white house ta nuna matukar rashin jin dadinta game da mafakar siyasa na wucin gadi da kasar Rasha ta baiwa Edward Snowden tsohon ma'aikacin leken asirin kasar Amurka,tana mai cewa tana tunanin matakin da za a dauka dangane da ganawar da aka shirya yinta a tsakanin shugabannin kasashen biyu a watan Satumba mai zuwa.

A lokacin ganawar sa da manema labarai kakakin na white house Jay Carney ya ce Amurka ta yi matukar bakin cikin ganin cewa Rasha ta dauki wannan matsayi duk da bukatarta bisa ga doka da ta bayyana a fili da a tasa keyar Snowden zuwa gida domin ya fuskanci hukuncin laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

Wannan matsayi in ji Mr Carney da Rasha ta dauka ya gurgunta cigaban da aka samu ta bangaren hadin gwiwa don inganta ayyukan tsaro da ya kara habaka tun lokacin harin bam da aka kai yayin wasan tseren Boston a watan Afrilun bana.

Snowden dai wanda ya dade yana fake a filin saukar jiragen sama tun shigar sa kasar ta Rasha a ranar 23 ga watan Yuni ya fita zuwa wani waje na sirri da zai zauna a cikin gari sakamakon ba shi mafakar siyasa ta wucin gadi da ma'aikatar kula da baki na kasar Rasha ta yi har na tsawon shekara daya. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China