in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya soke ganawarsa da Putin
2013-08-08 15:34:03 cri

Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta sanar a ran 7 ga wata cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya soke tattaunawar da ya shirya yi tsakaninsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a farkon watan Satumba a birnin Moscow, saboda tabarbarewar dangantaka tsakanin Amurka da Rasha sakamakon mafakar da Rasha ta baiwa tsohon mai leken asiri na kasar Amurka Edward Snowden

Kakakin fadar White House Jay Carney ya ba da sanarwa cewa, Amurka ta nuna rashin jin dadi sosai kan shawarar da Rasha ta yanka, wadda ta kasance matakin da Amurka ta yi amfani da shi wajen kimanta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Duk da haka, ya ce, Obama zai halarci taron koli na G20 da za a yi daga ran 5 zuwa 6 ga watan Satumba na shekarar bana a Sant-Petersburg na kasar Rasha.

Mai ba da taimako ga shugaban Rasha Yury Ushakov ya nuna a ran 7 ga wata cewa, Rasha ba ta ji dadin matakin da Obama ya dauka ba, amma ya ce, Rasha ta gayyaci Obama don kawo ziyara birnin Mascow, kuma Rasha za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da takwararta ta kasar Amurka kan wasu manyan batutuwa tsakanin bangarorin biyu da kuma tsakanin bangarori da dama. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China