in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin hakar ma'adanai na iya tallafawa wajen samar da wutar lantarki, in ji bankin duniya
2015-02-11 10:15:54 cri

Wani sabon rahoton da bankin duniya ya fitar, na yi nuni da irin rawar da kamfanonin hakar ma'adanai ka iya takawa, wajen samar da karin wutar lantarki, a kasashen dake kudu da hamadar Saharar Afirka.

Rahoton ya ce, idan har an dauki matakan da suka wajaba, ciki hadda hadin gwiwa tsakanin irin wadannan kamfanoni da kamfanonin samar da lantarki, ana iya samar da karin wutar lantarki daga hanyoyin da ba sa gurbata muhalli. Kaza lika hakan zai ba da damar magance karancin lantarki, wanda ke addabar a kalla kashi daya bisa uku na daukacin nahiyar Afirka.

Yankin kudu da hamadar Sahara, a cewar rahoton na bankin duniya, na samar da wutar lantarki da yawanta bai wuce gigawatt 80 ba a ko wace shekara, adadin da mutane biliyan daya da digo 1, dake kasashe 48 ke amfana daga gare shi.

Sai dai a cewar rahoton, kaso 2 bisa 3 na al'ummar wannan yanki na rayuwa ne babu wutar lantarki, yayin da ragowar dake da wutar ke ci gaba da fama da karancinta.

Bisa hasashe, bankin duniyar ya ce, muddin ba a dauki sabbin matakan magance wannan matsala ba nan da shekarar 2030, yawan al'ummun yankin dake fama da rashin wutar lantarkin zai yi matukar karuwa fiye da na yanzu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China