in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta Kudu ya taya jama'ar Sin murnar zuwan sabuwar shekarar rago
2015-02-10 20:07:55 cri
A yau ne, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya mika sakon alheri ga jama'ar kasar Sin dangane da shigar sabuwar shekara ta rago bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kana ya ce, yana sa ran bunkasuwar dagantakar dake tsakanin kasar Afirka ta Kudu da kasar Sin cikin yanayi mai kyau cikin sabuwar shekara mai zuwa.

Cikin sakon na shugaba Zuma, ya ce, shekarar rago ta gargajiyar Sin tana alamta zaman lafiya, lumana, hadin gwiwa, kwanciyar hankali, da ci gaban samun bunkasuwa, lamarin dake da muhimmiyar ma'ana ga jama'ar kasar Afirka ta Kudu, inda ya ce suna sa ran makoma mai haske , lumana da wadata cikin sabuwar shekarar da ke tafe.

Ya kuma bayyana fatansa na ganin bunkasuwar Afirka ta Kudu da Sin cikin hadin gwiwar kasashen biyu a wannan sabuwar shekara. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China