in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta Kudu ya taya kasar Sin murnar bikin bazara
2015-02-17 10:29:20 cri
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya taya al'ummar Sinawa dake zaune cikin kasarsa, dama wadanda ke sassan duniya daban daban, murnar zagayowar bikin bazara na shekarar rago bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.

Zuma ya ce, shekarar rago na alamta zaman lafiya, da jituwa, da kasancewa cikin yanayin lumana da wadata. Kana tana da babbar ma'ana ga daukacin al'ummar Afirka ta Kudu.

Zuma ya kara da cewa, an gudanar da bikin al'adun Afirka ta Kudu a kasar Sin a shekarar 2014, kuma za a gudanar da bikin al'adun Sin a kasar Afirka ta Kudu a bana. Ya ce kasashen biyu na taya juna murnar raya dangantakar zumunta dake tsakaninsu, kana kasar Afirka ta Kudu na da imani game da kara inganta dangantakar hadin gwiwar tattalin arziki tsakaninta da kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China