A nan gaba ne ake sa ran mika dokar ga majalisar ministocin kasar Afirka ta Kudun don yin muhawara a kan ta, kana daga baya a ji ra'ayoyin jama'ar kasar kan wannan doka, daga bisani kuma a mika ta ga majalisar dokokin kasar don ta zartas da ita, kana a karshe shugaban kasar zai sanya mata hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa, kayyade filayen da 'yan kasashen ketare za su mallaka wani batu ne da aka amince da shi a fadin duniya, kuma an tsara doka game da wannan lamari ne don tabbatar da tsaron yankunan kasa da batun samar da abinci a kasar Afirka ta Kudu, kana za a warware matsalar rashin daidaito kan rarraba filayen kasar bayan da aka kawar da tsarin mulkin mallaka da nuna wariyar launin fata da aka aiwatar a kasar na fiye da tsawon shekaru 300. (Zainab)