An fara taron a ran 11 ga wata, inda ministoci da masana da suka zo daga kasashen Sin, Brazil, India, Rasha da kuma Afirka ta Kudu suka tattauna kan batutuwan da suka shafi mata da yara, yin rigakafi kan cututuka masu yaduwa da cutar kanjamau, kaurar mutane daga karkara zuwa birane, tsufan al'umma, nuna bambanci ga maza da mata cikin kasuwannin neman aikin yi da dai sauransu. (Maryam)