Kafuwar bankin BRICS zai karfafa bunkasuwar kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa
A jiya Laraba 15 ga wata ne, Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana a birnin Fortalezan kasar Brazil cewa, kafuwar bankin musamman na tsimi da samar da ci gaba na kasashen BRICS da shirin samar da kudin da za a tanada don fuskanta wasu ayyukan gaggawa na kasashen BRICS zai taimaka wa kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da kasashe masu tasowa wajen samun bunkasuwar tattalin arziki.
Bugu da kari, Mrs. Rousseff ta jaddada a yayin taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na shida cewa, kafuwar bankin zai karfafa mu'amalar sha'anin kudi dake tsakanin kasashen BRICS, wanda zai ba da babbar gudumawa wajen raya hukumomi sha'anin kudi da kuma taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samun dauwamammen ci gaba yadda ya kamata cikin hadin gwiwa. (Maryam)