Ya yin wannan taro shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, kasashen BRICS, da kasashen nahiyar kudancin Amurka dukkansu kasashe ne masu tasowa da ke samun saurin ci gaba. Don haka ya yi kara da a kira gudanar da hadin gwiwa a fannin kasuwancin bangarorin.
Sauran shugabannin da suka halarci taron sun bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa, da cin moriyar fasahohi, da yin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da na nahiyar kudacin Amurka na da babbar ma'ana.
Kana a daya hannun kasashen nahiyar kudancin Amurka na maraba da yunkurin kasashen BRICS na kafa bankin raya kasa da tsarin ajiye kudi, tsarin da zai iya samar da karfin gwiwa ga kasashen duniya a fannin hada-hadar kudi, da kuma magance matsalar da fannin ke fuskanta.
Kaza lika Sun yi imani cewa, hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu zai taimakawa musu wajen samun bunkasuwa, tare da sa kaimi ga kafuwar tsarin dimokuradiyya, da zaman lafiya, da wadata a fadin duniya gaba daya.
An gudanar da taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS ne, da na kasashen nahiyar kudancin Amurka a birnin Brasilia a ranar 16 ga wata, inda shugaban Sin da sauran shwagabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, da kuma shugabannin kasashen nahiyar kudancin Amurka kamar Argentina, da Columbia, da Venezuela da dai sauransu suka halarta. (Zainab)