Shugabar asusun ba da lamuni na IMF Christine Lagarde, ta taya kasashe mambobin kungiyar BRICS murnar kafa asusun ajiyar kudaden tinkarar al'amuran gaggawa. Madam Lagarde wadda ta bayyana hakan a jiya Laraba ta kuma jinjinawa kasashen na BRICS, bisa kokarinsu na kiyaye ingantaccen yanayi a fannin kudi a duk duniya.
A cikin wasikar da ta aikewa shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, Madam Lagarde ta bayyana farin cikinta ga nasarar da aka samu daga taron kolin kungiyar kasashen na BRICS. Ta ce, IMF na raya dangantaka mai kyau da ko wace kasa daga kasashen BRISC, yana kuma fatan kara hadin kai da su.
Manazarta dai na nuni da cewa, a 'yan shekarun baya bayan nan, ba a cimma wata babbar nasara ba, a fannin kara ba da kason IMF ga kasashen da ke samun saurin bunkasuwa. Hakan dai ya kawo illa ga kwarewar IMF wajen samun kudade.
A hannu guda kuma asusun ajiye kudade na kasashen BRICS ya samar da wani sabon mataki, wajen tabbatar da tsaron harkokin kudi a duk duniya, matakin da ake sa ran cimma gagarumar nasara. Kaza lika asusun zai iya bada wata kariya da tabbaci a fannin hada-hadar kudi ga kasashe masu tasowa. (Danladi)