A yayin shawarwarin, Mr. Wang ya nuna cewa, ganawar tsakanin shugabannin kasashen BRICS da aka yi a bana a Fortaleza ta samar da sabon zarafi ga tsarin kungiyar. Don haka ya kamata bangarorin daban-daban mahalartan taron su yi amfani da wannan zarafi domin tsai da shirin hadin kan tattalin arziki nan gaba tsakaninsu.
Ministocin mahalartan taron sun kai da matsaya daya cewa, a wannan yanayin da ake ciki, ya kamata kasashen BRICS su kara hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su zurfafa dangantakar sada zumunci ta fuskar tattalin arziki da ciyar da hadin kai ta fuskar ciniki, tattalin arziki da zuba jari gaba. Ban da haka kuma, ya ce kamata ya yi a kara hadin kai ta fuskokin yaki da ta'addanci a duniya, magance cutar Ebola, matsalolin da suka shafi Palasdinu, da Ukraine da sauransu, da kuma kiyaye zaman lafiya da tsaron duniya tare. Kazalika, ya kamata a goyi bayan MDD da ta shirya bukukuwan tunawa da cikon shekaru 70 da aka kafa kungiyar, da kuma samu nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu, da dukufa kan kiyaye zaman oda na duniya mai adaci da daidaici karkashin tsarin mulkin MDD. (Amina)