in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya bukaci bangarori daban-daban na kasar Ukraine su mutunta yarjejeniyar Minsk
2015-01-19 16:06:46 cri
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayar da wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya damu sosai kan kazamin fadan da aka yi na neman kwace ikon filin saukar jiragen saman Donetskaya na kasar Ukraine, inda ya bukaci bangarori masu ruwa da tsaki su mutunta yarjejeniyar Minsk tare da tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce, fadan da aka yi na neman kwace filin jiragen saman Donetskaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, lamarin da ke nuna cewar, hakan keta yarjejeniyar da aka cimma ne a watan Satumbar bara. Mista Ban Ki-Moon ya nemi bangarori daban-daban da su cika alkawarin da suka dauka a cikin yarjejeniyar Minsk, kana su gaggauta daina yin fito-na-fito a tsakaninsu.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China