Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi yayin wata lacca a birnin Washington, inda ya bayyana muhimmancin karfafa dangantaka tsakanin Amurka da Sin.
Hong Lei ya ce, idan sassan biyu suka yi hadin gwiwa yadda ya kamata a matakan shiyya-shiyya da duniya baki daya, hakan zai taiamaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da Fasifik da ma duniya baki daya.
Kasar Sin na fatan yin aiki tare da Amurka wajen hanzarta aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma ta yadda za a gina sabuwar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu ba za su tsokani juna ba, mutunta juna da samun moriya tare don amfanin al'ummomin kasashen biyu da ma duniya baki daya. (Ibrahim)