Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yau yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa ta ce, kasar Sin na sa ido kan halin da ake ciki a kasar ta Burkina Faso.
Ta ce, kasar Sin na fatan dukkan bangarorin da batun ya shafa za su yi la'akari da muradun kasar da al'ummarta kana su warware dukkan bambance-bambance da ke tsakaninsu ta hanyar hawan teburin sulhu da tuntubar juna don ganin an maido da zaman lafiya da ci gaba a kasar.
Madam Hua ta bayyana cewa, har kullum kasar Sin daya tak a duniya na martaba manufofi biyar na kasancewa cikin zaman lafiya ta yadda za ta bunkasa dangankatar abokantaka da sauran kasashe. (Ibrahim)