in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Amurka sun tattauna ta wayar tarho
2013-12-16 12:33:29 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya buga waya a ranar Lahadi da yamma ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry domin tattauna dangantakar kasashen biyu, shawarwarin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palesdinu da kuma batun kasar Syria.

Da yake tabo cigaban dangantaka da kasashen biyu suke samu, mista Wang Yi ya bayyana cewa, shekarar 2014 za ta kasance muhimmiyar shekara ga kasashen biyu, tare da nuna fatan cewa, Beijing da Washington za su kara zurfafa shawarwari da dangantakarsu, domin fadada amincewa da juna, ta yadda za'a mai da hankali kan manyan batutuwan da ke janyo rabuwar kai tsakaninsu, da kuma karfafa sandarwa da dangantaka kan harkokin shiyya shiyya da na kasa da kasa.

A nasa bangare, mista Kerry ya jaddada niyyar Amurka ta yin aiki tare da kasar Sin domin kara hadin gwiwa da fadada musanya kan muhimman batutuwan shiyya shiyya da na kasa da kasa. Game da shawarwarin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palesdinu, Wang Yi ya ce, zai fara wata ziyarar aiki a yankin Gabas ta Tsakiya don kara kusanto bangarorin biyu kan teburin shawarwari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China