Hua Chunying ta ce, Sin ta bukaci Ghana da ta gudanar da bincike bisa dokoki yadda ya kamata, da dakatar da kame Sinawa a waje da yankunan hakar ma'adinai, da dakatar da ayyukan harin da wasu mutanen wurin suke kai wa Sinawan tare da kwace masu dukiyoyi, da kuma tabbatar da tsaron Sinawa da suke son komawa gida Sin, da kiyaye kayayyakin ayyukan su da sauran dukiyoyin su bisa iyakacin kokari.
Yanzu dai an riga an saki duk Sinawa 169 da aka cafke a Ghana.(Fatima)