A lokacin ganawar, Mista Amissah-Arthur ya ce Ghana na son yin amfani da tallafin da kasar Sin ke ba ta, don samun wani ci gaban tattalin arziki wanda saurinsa zai kai na kasar Sin. Haka zalika, a cewar Mista Amissah-Arthur gwamnatin kasar Ghana za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.
A nasa bangaren, Mista Huang Xianyao ya ce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da jam'iyyar NDC ta Ghana, don haka tana fatan kara hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun 2, da ci gaba da kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.(Bello Wang)