Ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a shekarar 2014, gwamnatin tsakiyar kasar ta kebe kudin Sin Yuan biliyan 48, don kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar a yau Talata 1 ga watan Yuli, ta ce a shekara ta 2008 ne, gwamnatin tsakiya ta Sin ta fara kebe kudade musamman ga wasu manyan yankuna, da ke aikin kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai. Gwamnatin tsakiyar tana fatan ta hanyar ware wannan kudi na taimako ga gwamnatocin wurare daban daban, za a kai ga inganta kare yankuna, wadanda aka haramtawa harkar raya masana'antu, ciki har da yankin Sanjiangyuan na lardin Qinghai, da wuraren samar da ruwa a yankunan ayyukan jawo ruwa daga kudu zuwa arewa, da dai sauran yankunan kare hallitu na kasa, da ma wuraren da aka killace kayan tarihi na al'adu, don hana gurbatar su, da kuma magance matsalar da suka iya fuskanta.
Yawan wuraren da gwamnatin tsakiya ta Sin ta kebe kudi domin kare su, ya zuwa wannan shekara ta 2014, sun kunshi gundumomi da garuruwa 512, ciki har da gundumomi 20 da suka kasance ganuwar kare hallitu ta lardin Hebei, da ke kewayen biranen Beijing da Tianjin, da tsaunin Qomolangma na jihar Tibet. (Danladi)