in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ajandar MDD bayan shekarar 2015 za ta mai da hankali kan kare muhalli
2014-06-23 10:54:37 cri

MDD ta bayyana jiya Lahadi ranar 22 ga wata a birnin Nairobin kasar Kenya cewar, ajandar bayan shekara ta 2015 za ta fi mai da hankali ne a kan al'amurran kare muhalli, a daidai kuma lokaci guda a shekarar ta 2015, MDD za ta dakatar da muradun wannan karni MDG, saboda shirin ya cinye shekarun da aka kayyade mashi.

Babbar mai ba da shawara ta musamman ga darektan manufofin ci gaba masu dorewa SDGs, Maryam Niamir-Fuller, ta shaidawa wani taron manema labarai a Nairobi cewar, wayar da kan jama'a zai tabbatar da cewar, kokarin da ake yi na ci gaba ba za su gurbata yanayi ba.

Maryam ta kara da cewar, dukanin kasashe suna sane da cewar, kare muhalli ba zai kawo tafiyar hawainiya ba ga bunkasar tattalin arziki., ta kara da cewar, a shekarar badi za'a fara amfani da manufofin ci gaba masu dorewa, wadanda su ne za su samar da ginshiki da zai samar da taswirar ajandar duniya a shekaru 15 masu zuwa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China