Rahoton ya yi nazari ne kan kasashe 142 a duniya, inda aka duba fannoni hudu wato kiwon lafiya, bada ilmi, tattalin arziki da kuma siyasa.
A shekarar 2006 ne dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya ya fara gabatar da irin wannan rahoto. Alkaluman da aka gabatar a shekaru 9 da suka gabata sun bayyana canjin da aka samu wajen nuna adalci a tsakanin maza da mata a kasa da kasa, tare da bambance-bambance da ake fuskanta a tsakaninsu a wannan fanni. (Zainab)