Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana bukatar baiwa mata cikakkiyar kariya a yankunan dake fama da rigingimu, tare da sanya su cikin shirin wanzar da sulhu, da ma manufofin yaki da ta'addanci.
Mr. Liu wanda ya bayyana hakan yayin zaman kwamitin tsaron MDDr ya ce, akwai bukatar kasashe duniya su yi hadin gwiwa, wajen baiwa mata irin kariyar da ta dace, duba da yadda su kan fuskantar tarin kalubale da cin zarafi iri-iri a lokutan yaki ko tashe-tashen hankula.
Wakilin kasar ta Sin ya kara da jaddada muhimmancin magance wannan matsala tun daga tushe, yana mai bayyana bukatar hadin kai wajen baiwa matan da suka tsinci kan su cikin wannan halin tallafin jin kai tare da cikakkiyar kariya ga rayukansu. (Saminu)