Majalisar gudanarwar kasar Sin a ranar Laraban nan ta sanar da cewa, za ta kafa wani asusu na yuan biliyan 40, kwatantacin dalar Amurka biliyan 6.54, wanda zai ba da taimako ga kirkire kirkire a kokarin da take yi na ingiza wannan bangaren.
Wannan shirin na gwamnati yana da zummar jawo hankalin masu zuba jari, a cewar wata sanarwa da aka fitar bayan taron majalisar gudanarwar kasar karkashin shugabancin firaministan kasar Li Keqiang.
Bayan kaddamar da wannan shiri ga al'umma, kamfanonin kula da asusu da dama za'a zaba domin tafiyar da shi, kuma za'a ba su izinin shawarar a kan zuba jari a ciki.
Wannan shiri dai yana da manufar ingiza ci gaban masana'antu da kara kwazo a ciki.
Taron na ranar Laraba ya kuma yi alkawarin inganta ayyukan ci gaban ciniki, da ba da kafa ga bangaren kudi, ilimi, al'adu, kiwon lafiya da masana'antu, in ji sanarwar. (Fatimah)