in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa fiye da miliyan 97 ne ke amfani da fasahar yanar gizo ta 4G kan layukan salula
2015-01-28 16:09:32 cri

Ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta fidda wani rahoto a jiya Talata 27 ga watan nan, game da bunkasuwar sana'ar sadarwar wayoyin salula na shekarar 2014.

Rahoton da ya nuna cewa wannan sashe na samun bunkasuwa kwarai, sakamakon karuwar bukatun jama'a a wannan fanni a bara, musamman ma fasahar yanar gizo ta salula ta 4G, wadda ta samu ci gaba fiye da yadda aka yi tsamani, inda yawan Sinawa dake amfani da ita ya kai miliyan 97.28.

Bisa kididdigar da ma'aikatar ta bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2014, yawan mutanen da suke amfani da yanar gizo ya kai miliyan 583, cikin wannan adadi mutane da suke amfani da yanar gizo ta salula ya karu zuwa kaso 45.3 cikin dari, kana yawan lokacin da ake amfani da shi wajen shiga yanar gizo ya yi matukar karuwa. Rahoton ya kuma nuna cewa, daga wannan adadi, kason da ake amfani da shi ta hanyar salula ya kai kashi 86.8 cikin dari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China