Haka kuma, a madadin shugaba, gwamanti da jama'ar kasar Sin, Qiangba Puncog ya taya wa kasar Zambia murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kan kasa, ya ce, shekarar bana ita ce cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Zambia, kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Zambia wajen karfafa hadin gwiwar kasashen biyu daga dukkan fannoni, karfafa mu'amalar dake tsakanin hukumomin majalisun kasashen biyu, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Kasar Zambia ta nuna godiya ga halartar wakilan kasar Sin a bikin, ta kuma bayyana fatanta wajen yin hadin gwiwa da kasar Sin don ci gaba da samun kyawawan sakamako bisa hadin gwiwar kasashen biyu. (Maryam)