Bisa wani labarin da shafin intanet na fadar shugaban kasar Rasha ya fitar, an ce, shugabannin biyu sun yi musanyar ra'ayi dangane da rikicin kasar Ukraine ta wayar tarho, inda shugaba Putin ya jaddada cewa, babban aiki a halin yanzu shi ne a kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta yadda ya kamata, da kuma nuna goyon baya ga kasar Ukraine kan aikin farfado da tattalin arziki a yankin kudu maso gabashin kasar. Haka kuma, shugaba Putin ya kara da cewa, ya kamata gwamantin kasar Ukraine ta yi shawarwarin kai tsaye tare da wakilan yankin Donbass na jihar Donetsk da jihar Luhansk.
Bugu da kari, shugabannin kasashen biyu sun jaddada cewa, ya kamata a ciyar da aiwatar da yarjejeniyar Minsk gaba, da kuma ciyar da shawarwarin dake tsakanin ministocin wajen kasashen Ukraine, Rasha, Faransa da kuma Jamus gaba. (Maryam)