in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan bangarorin da rikicin Ukraine ya shafa su warware matsalarsu ta hanyar zaman lafiya
2015-01-12 20:24:52 cri
Rahotannin na cewa, a yau ne ake sa ran ministocin kasashen Rasha, Ukraine, Jamus da kuma Faransa za su gana a birnin Berlin na kasar Jamus, inda za su tattauna yanayin da ake ciki a kasar Ukraine don share fagen ganawar wasu shugabanni hudu a birnin Astana na kasar Kazakhstan dangane da shirin shiga-tsakani na Normandy.

Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin tana maraba da bangarorin da abin ya shafa su warware matsalar ta hanyar siyasa, kuma Sin tana fatan za a cimma nasarar shimfida zaman lafiya, tsaro, zaman karko a kasar Ukraine cikin sauri tare da ciyar da bunkasuwar kasar gaba, ta yarjejeniyoyin Normandy, Minsk da sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China