Rahotanni daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha na cewa, ministoci hudu sun jaddada bukatar gaggauta sake kiran taron wanzar da ci gaba, na tawagar kasar Ukraine, da kungiyar tsaro da hadin gwiwar kasashen Turai, da kuma kasar Rasha.
Kaza lika ministocin hudu sun tattauna kan ci gaban shawarwarin da kasashen suke gudanarwa da bangarori daban daban da wannan batu ya shafa.
Ya zuwa yanzu dai bangarori daban daban da batun kasar ta Ukraine ya shafa, sun amince da a ci gaba da ba da taimako wajen warware rikicin kasar ta Ukraine a siyasance.
Bisa kididdigar da hukumar MDD mai lura da wannan batu ta fitar, alkaluma sun nuna cewa, daga tsakiyar watan Afrilun bara ya zuwa yanzu, rikicin gabashin kasar ta Ukraine ya hallaka akalla mutane 4707, yayin da wasu sama da 10,000 suka jikkata. (Maryam)