Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na "Interfax Ukraine news" ya fitar, an ce Poroshenko ya yi jawabi ga kafofin watsa labarun kasar daga jihar Zhitomir dake tsakiyar kasar, inda ya bayyana ra'ayinsa na tabbatar da zaman lafiya ta hanyar diplomasiya a yankunan dake gabashin kasar.
Bisa kuma wannan kuduri ne aka gudanar da shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Ukraine, da Rasha, da Jamus, da kuma Faransa. Aka kuma gudanar da taron share fage a ranar 5 ga watan nan a Berlin.
Haka zalika Poroshenko ya jaddada cewa, shekarar 2015 za ta kasance shekarar cimma nasarori da wanzar da zaman lafiya. Matakin da ke nuna bukatar rundunar soji mai nagarta da kwarewa, da ma na'urori masu inganci, da kuma mai kaunar kasa. (Bilkisu)