Madam Hua ta bayyana ta'aziyyar kasar akan wannan babban rashin ga gwamnati da al'ummar kasar Saudiyya, tana mai bayyana marigayi Sarkin a wani Shugaba na gari wanda ya sadaukar rayuwar sa domin inganta cigaban kasa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya kara masa martaba a gida da kasashen waje.
Ta ce marigayi Sarkin ya kasance mai mai da hankali akan ingiza dangantakar sada zumunci tsakanin kasar Saudi Arabiya da Sin, ya bayar da gudunmuwa kwarai wajen zurfafa wannan zumunci da hadin gwiwwa inji Madam Hua.
An dai haifi Marigayi Sarki Abdallah Ibn Abdulazeez ne a shekara ta 1924, ya rasu a daren alhamis wayewar garin jumma'ar nan bayan jinyar sanyin hakarkari da yayi fama dashi kuma yake kwance a asibiti tun a watan Decembar da ta wuce.
Tuni aka sanar da sunan Kanin sa mai jiran gado Yarima Salman bin Abdulaziz Al Saud a matsayin sabon Sarki sannan aka nada Yarima Muqrin bin Abdulaziz Al Saud a matsayin sabon mai jiran gado.