Sun Zhen ya jaddada cewa, batun sauyin yanayi ya kawo mummunan kalubale ga zamantakewar al'umma, kuma ya kamata a kara kokarin wajen yaki da wannan matsala. Mista Zhen ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta kara karfi don aiwatar da manufar raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, sannan kuma dole ne al'ummar kasar su bada hadin kai wajen raya kasa bisa tushen kiyaye muhalli.
A kwanan baya, majalisar gudanarwa ta bayar da shirin yaki da gurbataciyyar iska karo na farko, don nuna anniyar gwamnatin Sin wajen yaki da gurbatacciyar iska, inda aka yi alkawarin cewa, bayan da aka yi kokari har na tsawon shekaru 5, za a yi kokarin don kyautata ingancin yanayi da rage matsalar gurbataciyyar iska.
Ban da wannan kuma, kwararrun kasashen waje su ma sun mai da hankali sosai game da aikin kiyaye muhallin halittu a biranen kasar Sin. Shugaban kwamitin yin amfani da makamashi mai tsabta na kasa da kasa, mista Gustav Grob ya ba da shawara cewa, yayin da ake yin hadin gwiwa da kasar Sin, ya kamata a kara lura kan batun kiyaye muhalli.(Bako)